ABNA24 : Birgediya janar Heydari ya kuma ci gaba da cewa; An sami gagarumin sauyi a cikin yadda ake tafiyar da aikin soja da hakan ya mayar da rundunar sojan Iran zama mai karfin kai farmaki a kowane lokaci.
Birgadiya janar Heydari dai yana yin jawabi ne a wurin gudanar da rawar dajin soja ta “Wilaya 99” ya kuma ce; A yayin atisayen sojan an yi gwaje-gwaje masu tasirin gaske,haka nan salon kai hare-hare a cikin yanayin daban-daban da suka hada dare da rana.
342/